Isra’ila: An sako Falasɗinawa 90 da aka yi garkuwa da su a cikin shirin tsagaita wuta na Gaza

 


Isra’ila ta sako Falasɗinawa 90 da aka yi garkuwa da su a matsayin wani ɓangare na matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas.

Dukkan Falasɗinawan da aka sako sun fito daga gidan yarin Ofer da ke cikin Yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, a ranar Litinin, in ji Hukumar Gidajen Yarin Isra’ila.

An ɗauke su da motocin bas zuwa garin Beitunia da birnin Ramallah a Yankin Yammacin Kogin Jordan.

Daruruwan Falasɗinawa sun cika titunan Beitunia da Ramallah cikin murna, suna ɗaga tutocin Falasɗinu tare da rera taken nuna farin ciki.

Yayinda Falasɗinawan suka ɗaga tutocin gwagwarmaya daban-daban, ciki har da na Hamas da Islamic Jihad.

Matan da aka sako daga tsarewa suna cikin bas suna murmushi tare da nuna alamar nasara.

Falasɗinawa 90 da aka sako da sanyin safiyar Litinin – dukkan su mata da yara – su ne na farko daga cikin sama da 1,000 da ake sa ran za a sako a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko, a madadin Isra’ilawa 33 da aka kama a Gaza.

Rahoton AFP ya bayyana cewa, sama da 230 daga cikin Falasɗinawan da za a sako za a kori su daga ƙasar nan da nan bayan an sake su.

Su wanene aka sako daga cikin fursunonin Falasɗinawan?

An sako Falasɗinawa 90 a ranar farko ta yarjejeniyar tsagaita wuta, waɗanda dukkan su mata ne ko yara.

Daga cikin waɗanda aka sako har da Khalida Jarrar, ’yar siyasa kuma shugaba a ƙungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine (PFLP) a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Hukumomin Isra’ila sun taɓa tsare Jarrar sau da yawa a baya bisa zargin “tunzuri” dangane da kalamanta kan mamayar Isra’ila.

Falasɗinawan da aka sako sun haɗa da yara, waɗanda wasu daga cikinsu aka tsare ba tare da ƙayyadaddiyar lokaci ba saboda jifa da duwatsu ga sojojin Isra’ila.

Yawancin Falasɗinawan da ake tsarewa na fuskantar tsarewa na mulki, wanda wata dabara ce da Isra’ila ke amfani da ita don tsare mutane ba tare da gabatar da tuhuma ba.

Isra’ila ta sanar a baya cewa za ta sako Falasɗinawa 737 a cikin kwanaki 42 na farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.

Hamas ta tabbatar da mika wasu Isra’ilawa uku da aka kama ga wakilan Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Duniya (ICRC).

“Red Cross ta sanar da cewa an mika mutanen uku da aka kama gare su kuma suna kan hanyarsu zuwa wurin sojojin IDF da jami’an ISA a Gaza,” in ji sojojin Isra’ila a wata sanarwa, suna amfani da gajerun sunaye na sojojin Isra’ila da Hukumar Tsaron Isra’ila.

Mutanen ukun – Romi Gonen, Emily Damari, da Doron Steinbrecher – su ne na farko daga cikin mutane 33 da ake sa ran ƙungiyar gwagwarmaya za ta sako a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Hamas za ta saki mutum huɗu a rana ta bakwai na tsagaita wuta, sannan saura 26 za a sako a cikin makwanni biyar masu zuwa.

Ana kuma sa ran za a sako waɗanda aka kama daga ƙasashen ƙetare, ciki har da Amurkawa, a ƙari ga Isra’ilawa 33, kamar yadda CNN ta rawaito, tana ambaton majiyoyi da suka san lamarin.

Post a Comment

Previous Post Next Post