McDonald’s ta yi hasarar fiye da dala biliyan $7 sakamakon yajin sayayya (Boycott) saboda goyon bayanta ga Isra’ila

 


McDonald’s ta yi hasarar fiye da dala biliyan $7 sakamakon yajin sayayya da masu goyon bayan Falasɗinu suka ƙaddamar a duniya saboda ta'addancin Isra'ila a Gaza.

Wani rahoto na kafofin watsa labarai na kuɗi na Isra'ila ne ya tabbatar da waɗannan hasarorin.

Yajin sayayya, Divestment, da kuma takunkumai (BDS), wani yunƙuri na jama'a, ya sa McDonald’s a gaba saboda goyon bayanta ga yakin kawar da al’umma da Isra’ila ke yi a Gaza.

Yajin sayayyar kayayyakin Isra'ila ya fara a watan Oktoba 2023 bayan McDonald’s a yankunan Falasɗinu da Isra’ila ta mamaye sun sanar da ba da dubban abinci kyauta ga sojojin Isra’ila.

Sanarwar ta jawo tirjiya nan take, musamman a kasashen musulmi masu goyon bayan Falasɗinu, tare da kiran a yi watsi da kayayyakin gwamnatin wariyar launin fata.

Yajin sayayyar McDonald’s saboda goyon bayanta ga Isra'ila ya yi mummunar illa ga tallace-tallace a yankin Larabawa da duniya ta Musulunci.

Sakamakon kasuwanci ya nuna tasirin yajin sayayyar a Gabas ta Tsakiya bayan McDonald’s ta sanar da ba da abinci kyauta ga sojojin Isra’ila.

Wasu gidajen cin abinci na Franchise a kasashen da ke da manyan al’ummomin Musulmi sun yi Allah-wadai da wannan matakin, kuma yajin sayayyar ya yadu daga Masar da Jordan zuwa wasu yankuna, ciki har da Malaysia.

Babban Jami’in Kula da Kuɗi na wannan kamfanin abincin, Ian Borden, ya bayyana cewa a cikin sa’o’i kaɗan, yajin sayayya ya haifar da mummunar hasarar kuɗi.

Wannan labarin ya zo bayan furucin Borden cewa rikicin da ke ci gaba da gudana a Gabas ta Tsakiya da raguwar buƙatu a China za su haifar da saukar tallace-tallace na duniya ga kamfanin.

Kamfen ɗin yajin sayayya kan kayayyakin Isra’ila saboda yaƙin Gaza ya yi mummunar illa ga manyan kamfanonin abinci na Yammacin duniya cikin watannin da suka gabata.

McDonald’s na daya daga cikin Franchise na Yammacin duniya da ake yi wa kamfen na yajin sayayya saboda goyon bayan da suke ba sojojin mamaya na Isra’ila.

Sauran kamfanonin Amurka, ciki har da Starbucks, Burger King, KFC, Pizza Hut, da Papa John’s, tare da wasu alamu kamar Coca-Cola, Pepsi, Wix, Puma, da Zara da ke da goyon baya ga Isra’ila ko kuma dangantakar kuɗi da ita sun fuskanci suka da kiraye-kirayen yajin sayayya.

Dubban masu sa kai a fadin duniya sun shiga yunƙurin BDS, wanda ke kira ga mutane da ƙungiyoyi a duniya su katse dangantakar tattalin arziki, al’adu, da ta ilimi da Tel Aviv don taimakawa wajen tallafa wa manufar Falasɗinu.

Yunƙurin ya yi nasarar jawo mummunar hasarar tattalin arziki ga gwamnati, wanda ƙungiyoyin masu goyon bayan Isra’ila suka kira “barazana ga wanzuwar su.”

Post a Comment

Previous Post Next Post