Ana sa ran Isra’ila za ta saki Falasdinawa 200 a kan fansar mata sojojin Isra’ila hudu, in ji wani jami’in kafar yada labarai na Hamas.
An sanar da hakan ne a ranar Talata daga bakin Nader Fakhouri, jami’i a Ofishin Watsa Labarai na Fursunoni da ke karkashin Hamas.
Fakhouri ya ce, “Za a fara kashi na biyu na matakin farko na yarjejeniyar kungiyoyin gwagwarmaya na Falasdinu da mamayar Isra’ila a ranar 25 ga Janairu.”
“A ranar Asabar, gwagwarmayar za ta sanar da sunayen fursunonin Isra’ila da zata saki, sannan itama Isra’ila za ta bayar da jerin sunayen Falasɗinawan da zata saki.”
“Daga kan wadannan jerin sunayen biyu, za a fara aiwatarwa a zahiri a ranar Lahadi, 26 ga Janairu, inda za a saki fursunonin Falasdinu tare da mika fursunonin Isra’ila.”
Taher al-Nunu, wani jami’in Hamas, ya tabbatar da cewa za a saki mata Isra’ilawa hudu a kan fansar wani rukuni na Falasdinawa.
Zaman tsagaita wuta ya fara aiki a ranar 19 ga Janairu. Isra’ila ta saki Falasdinawa 90 da aka kama a wani bangare na matakin farko na zaman tsagaita wutar. Dukkansu an sako su daga gidan yari na Ofer a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye a ranar Litinin.
Hamas ta ce tana da kwarin gwiwar bin yarjejeniyar zaman tsagaita wutar Gaza.
Shugaban Amurka Trump ya ce ba shi da kwarin gwiwar cewa zaman tsagaita wutar zai dore tsakanin Isra’ila da Gaza.
Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasarar cimma yarjejeniyar zaman tsagaita wutar, yanzu ya ce ba shi da tabbacin cewa zaman tsagaita wutar Gaza zai dore yayin da ya shiga rana ta uku.
Da yake mayar da martani ga tambayoyin ‘yan jarida, Trump ya ce: “Ba yaƙinmu ba ne, yaƙinsu ne. Amma ba ni da tabbaci.”
Trump ya bayyana a fili cewa zai goyi bayan Isra’ila, kuma a daya daga cikin matakan farko da ya dauka a matsayin shugaban kasa, ya janye takunkumin da aka sanya wa masu tsattsauran ra’ayi na Isra’ila da ke zaune a yammacin gabar kogin da gwamnatin Biden ta kakaba kan hare-haren da suke kai wa Falasdinawa.
Amma Qatar, wacce ta taimaka wajen shiga tsakani a yarjejeniyar zaman tsagaita wutar, ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zartar da kuduri kan aiwatar da yarjejeniyar zaman tsagaita wutar gaba daya.
Wakiliyar Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Sheikha Alya Ahmed bin Saif Al Thani, ta yi kira ga wannan hukuma ta kasa da kasa da ta tabbatar da nasarar yarjejeniyar, ciki har da zartar da kuduri mai tilas da ya shafi hakan.
Da take jawabi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Al Thani ta sake jaddada adawar Qatar da duk wani yunkuri na “hana samun mafita mai dorewa ga matsalar Falasdinawa, ciki har da yunkurin kwace yankunan Falasdinawa da keta hurumin wuraren ibada masu tsarki.”