Isra'ila ta kai mummunan hari kan birnin Jenin; Hamas tayi kira a da a Motsa

 


Sojojin Isra’ila sun kashe akalla Palasɗinawa takwas tare da raunata wasu 35 a wani hari da suka kai kan birnin Jenin na yankin Yammacin Kogin Jordan da ke karkashin mamaya, lamarin da ya sa ƙungiyar Hamas ta kira matasa Palasɗinawa su tashi tsaye gaba ɗaya don yakar sojojin mamayar.

Kafofin watsa labarai na Palasɗinu sun bayyana cewa sojojin Isra’ila, tare da tallafin jiragen sama masu saukar ungulu, sun kutsa cikin Jenin da sansanin ‘yan gudun hijirarsu a safiyar Talata bayan wasu hare-haren jiragen sama mara matuƙa.

Mai magana da yawun rundunar tsaron Palasɗinu, Anwar Rajab, ya ce sojojin Isra’ila sun “buɗe wuta kan fararen hula da jami’an tsaro, inda suka raunata wasu fararen hula da jami’an tsaro da dama, ɗaya daga cikinsu yana cikin mawuyacin hali.”

Rundunar sojojin Isra’ila ta tabbatar cewa sojojinta, ‘yan sanda da hukumomin leƙen asiri sun fara wani aikin da Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana a matsayin aiki “mai girma kuma mai muhimmanci” don “ƙarasa ta’addanci.”

Harin da aka kai Jenin, inda sojojin Isra’ila suka gudanar da farmaki da hare-hare masu yawa cikin shekara guda, ya zo ne kwana biyu kacal bayan fara tsagaita wuta da ake jira tsawon lokaci tsakanin Isra’ila da ƙungiyar gwagwarmaya ta Palasɗinu, Hamas.

Hamas ta bayyana a wata sanarwa cewa mutanen Gaza “suna jimamin shahidan Jenin da suka fadi sakamakon hare haren da 'yan mamaya suka haddasa.”

Ƙungiyar gwagwarmaya ta kuma kira matasan Jenin masu tawaye da su tashi tsaye tare da ƙara matsa kaimi wajen fafatawa da sojojin Isra’ila.

Hamas ta ce farmakin da “ 'yan mamaya suka kaddamar a Jenin zai ci tura, kamar yadda dukkan sauran hare-harensu na baya kan mutanenmu suka ci tura” a Gaza.

Ƙungiyar gwagwarmaya, wadda ta yaƙi sojojin Isra’ila na tsawon kwanaki 741 a Gaza, ta ce farmakin da ta kai a watan Oktoba 2023 kan yankunan mamaye ya zama "ƙarshe ga rushewar mulkin Isra’ila."

Post a Comment

Previous Post Next Post