Rahotanni: 'Yan Sahayoniya sun Sake kai Hari a Masallacin Al-Aqsa


IRNA ta ruwaito cewa Daruruwan Yahudawan sahyuniya sun kaddamar da sabon farmaki kan masallacin Al-Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA sun labarta cewa, sun nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, wasu da dama daga cikin mazauna kasar Isra’ila sun kaddamar da wani sabon hari a kan masallacin al-Aqsa ayau Alhamis.

A rana ta uku ta Idin Ƙetarewa (Passover), wasu gungun mabiya yahudawan sahyoniya sama da 430 sun mamaye masallacin al-Aqsa.

Ma'aikatar da ke kula da da'awar Musulunci a Palastinu ta bayar da rahoton cewa, a yayin farmakin 'yan matsugunan sun gudanar da ayyukan ibada na Talmud, inda suka yi ta yawo a farfajiyar Al-Aqsa.

A halin da ake ciki sojojin mamaya na Isra'ila sun sanya takunkumi mai tsauri ga Falasdinawa masu ibada, inda suke duba takardun shaidarsu a kofar birnin Quds, tare da hana da yawa daga cikinsu shiga masallacin.

Post a Comment

Previous Post Next Post