Masu zanga-zanga a Turai sun yi kira da a kawo karshen kisan kare dangi a Gaza



IRNA ta ruwaito cewa Dubban masu zanga-zanga ne suka cika kan tituna a biranen Turai da dama, suna bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu a Gaza tare da yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a can.

An gudanar da gangamin ne a Berlin babban birnin kasar Jamus, babban birnin kasar Ireland, da kuma birnin Geneva na kasar Switzerland a ranar Asabar, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

A birnin Berlin kusan mutane 2,000 ne suka yi maci a majalisar dokokin tarayya Bundestag, inda suka nuna bacin ransu ga gwamnatinsu na goyon bayan kisan kiyashin da ake yi a Gaza ta hanyar sayar wa Isra'ila makamai.

Sun yi ta rera taken "Jamus tana ba da kudade, Isra'ila na kai harin bam", da "Babu makami ga Isra'ila."

Har ila yau Jamusawan na ɗauke da alluna masu ɗauke da alamun "A matsayin Yahudawa, muna kira da a kawo ƙarshen goyon bayan kisan kiyashi".

A birnin Geneva, masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu sun taru a dandalin Place de Neuve, inda suka yi maci a kan titunan birnin kafin su kammala taronsu a wajen ofishin MDD.

Kamar Jamusawa, masu zanga-zangar a Geneva kuma sun rera taken yin Allah wadai da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan kisan kiyashin da take yi a Gaza, tare da yin kira da a tsagaita bude wuta nan take.

Masu zanga-zangar sun kuma rera taken nuna adawa da shugaban Amurka Joe Biden kan goyon bayansa ga gwamnatin Isra'ila da Firayim Minista Benjamin Netanyahu.

Kuma a birnin Dublin, jama'a sun halarci taron gangamin hadin kan Falasdinawa na Ireland.

Sun yi kira da a dakatar da hare-haren Isra'ila a Gaza, kuma sun bukaci kauracewa gwamnatin "wariyar launin fata".

Jama'a a duk faɗin Turai sun gudanar da taruka masu yawa don nuna goyon baya ga Gaza tun lokacin da yankin Falasɗinawa ya fuskanci mummunan yakin Isra'ila a farkon Oktoba.

Turawa sun fusata da goyon bayan siyasa da soja da gwamnatocinsu ke ba gwamnatin Isra'ila.

Akalla mutane 34,049 yawancinsu mata da yara ne aka kashe a munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza tun bayan yakin.

Post a Comment

Previous Post Next Post