Muhimmancin Watan Rajab Da Ayyukan Shi

@ YAA MAHDI @


 Ku sani cewa bayan watannin Sha’aban da Ramadan, watan Rajab yana da falala mai girma, kamar yadda ruwayoyi da dama suka zo a kan falalar wannan wata.  Sannan kuma an ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: “Lallai Rajab Watan Allah ne mai girma.  Babu wani watan da zai kai wannan wata mai alfarma da nagarta. Yaqar mushrikai a wannan wata haramun ne. 
 
 Hakika Rajab watan Allah ne, Sha’aban watana ne, kuma watan Ramadan watan mutanena ne.  Don haka idan mutum ya Azumci yini daya ga wannan wata, to zai samu yardar Allah Madaukakin Sarki, kuma za'a kareshi daga fushinsa, kuma Za'a rufe masa kofofin wuta.”
 
 Haka nan Imam Musa bn Ja’afar al-Kazim (a.s) ya ce: “Idan mutum ya azumci yini ɗaya a cikin Rajab, wuta za ta nisance shi da tafiyar shekara guda.  Wanda ya azumci kwanaki uku, hakika ya sami Aljannah”.
 
 Haka nan an ruwaito Imam (a.s.) yana cewa: “Rajab (sunan) kogi ne a cikin Aljanna wanda ya fi madara fari Kuma yafi zuma Zaqi.  Don haka idan mutum ya azumci ko da yini guda a cikin Rajab, Allah Ta’ala zai bashi damar sha daga wannan kogin”.
 
 Imam Ja’afar Sadik (a.s.) ya ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: “Rajab wata ne na neman gafara ga al’ummata;  Don haka ku yawaita istigfari a cikin wannan wata fiye da yadda kuke yi a sauran watanni, domin Allah madaukakin sarki mai gafara ne kuma mai jin kai.  Ana siffanta wannan wata a matsayin wata mai falala, domin ana zubowa Al'umma ta rahama a cikinsa sosai.  Don haka sai ku yawaita wannan addu'ar kamar haka:
 
 اَسْتَغْفِرُ اللهَ وَ اَسْاَلُهُ التَّوْبَةَ.

 A wata ruwaya mai girman gaske Ibn Baabwayh ya nakalto Salim yana cewa: Na taba ziyartar Imam Sadik (a.s.) a karshen watan Rajab.  Da idanunsa suka juyo gareni, sai ya ce, “Shin ka azumci wata rana a cikin wannan wata, Salim?
 
 “A’a, ban samu ba,” na amsa.
 
 "Ka rasa lada mai girma," in ji Imam (a.s.). 
 
 “Irin wannan lada mai girma da babu mai iya bayarwa sai Allah Ta’ala.  Lallai wannan wata Allah Ta'ala ya fifita shi akan sauran watannin da suka gabata, wanda kuma ya sanya darajarsa (watan) tazama Mai girma, kuma hakika (Allah) ya girmama masu azumi a cikinsa".
 
 Sai na ce, “Ya dan Manzon Allah, idan na azumci sauran kwanakin watan Rajab, shin za a ba ni wani abu daga cikin ladan da aka yi wa masu azumi a cikinsa?
 
 Imam Sadik (a.s.) ya amsa masa da cewa, “Saurara Salim!  Idan mutum ya azumci ranar karshe ta wannan wata, to wannan zai kare shi daga Radadin mutuwa, da firgicin tashin kiyama, da Azabar kabari.  Amma wanda ya azumci kwanaki biyun karshen wannan wata, wannan zai ba shi damar wuce gadar (sirat) cikin aminci.  Amma wanda ya azumci kwanaki ukun karshe na watan, za a amintar da shi a ranar Firgici mai girma daga dukkan fitinun da ke cikinta, sannan kuma a kubutar dashi daga wuta”.
 
 Daga karshe, ku sani cewa yin azumin watan Rajab gaba daya yana kawo falala mai girma.  Sai dai kuma an ruwaito cewa wanda ya kasa yin azumin watan Rajab, yana iya yin wannan addu’ar Mai Zuwa kamar haka sau dari a kowace rana a cikin Rajab.
 
 سبحان الاله الجليلجن لا ينبن لا ينبن الاعز الاعز الاعز الال.

_Nasir Hassan Kankia

Allah Madaukakin Sarki kaba Jagora Lafiya, Katsareshi daga Sharrin Maqiya Ka kare mana Imanin Mu, Ka bamu juriya da Sabati a Addinin nan kuma ya Rabbi kasa damu Za'ayi. 

Kada ku manta Kuyi Like akan Page ɗin mu na Facebook Mai Suna YAA MAHDI , sannan kuyi Following na Website ɗin mu Domin samun Sabbin Posting ɗin mu, Mun Gode.

Idan da wani gyara ko shawara to Kuyi shi a comment, sannan Kuyi like akan wannan post sannan Kuyi share domin 'yan uwa su amfana. 

Post a Comment

Previous Post Next Post